Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : na kasar Iran ya nakalto Abul Fadl yana fadar haka, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar haramtacciyar kasar Isra’ila ta na yakar kasar Aljeriya ta kasar Morocco ne. Don haka majalisar dokokin kasar Aljeriya ta dauki matakin katse hulda da kasar ta Morocco.
A ranar Talatan da ta gabata ce ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramalan Lamamra ya bada sanarwan katse huldar jakadanci da kasar Morocco saboda rawar da take takawa wajen kutsawar HKI cikin nahiyar Afirka.
Kasar Aljeriya dai ta na jagorantar wasu kasashen Afirka don fitar da HKI daga kungiyar tarayyar Afirka (AU), wacce shuwagabannin kungiyar ba tare da neman shawarar kasashen nahiyar ba suka bata mamba mai sanya ido a cikin kungiyar.
342/